Gobe Ba Aiki A Kano: Hutun Sabuwar Shekarar Musulunci 1447
Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana ranar Alhamis, 26 ga Yuni, 2025 a matsayin ranar hutun murnar Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1447 bayan Hijira.
Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana ranar Alhamis, 26 ga Yuni, 2025 a matsayin ranar hutun murnar Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1447 bayan Hijira.
Wata Babbar Kotu a Jihar Kano, ta yanke wa wasu mutum shida hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 120, bisa samun su da laifin satar yara da kuma sayar da su. Mutanen da aka yanke wa hukuncin sun haɗa da Mercy Paul, Ebere Ogbono, Emmanuel Igwe, Loise Duru, Monica Oracha, da Chinelo Ifedigwe. An […]
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya yi kakkausar suka tare da yin Allah-wadarai da kisan gillar da aka yi wa wasu matasa biyu ‘yan jihar a garin Makurɗi, babban birnin jihar Benue. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce, a jiya Litinin ne da […]
Rundunar yan sandan jihar Kano ta ceto wani matashi mai suna Ibrahim Abubakar, mai shekaru 19 da yayi yunkurin kashe kansa ta hanyar fadowa daga kan allon talla (billboard) akan gadar Ado Bayero kusa da kan titin zuwa Maiduguri Road a jihar. Mukaddashin kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, DSP Hussaini Abdullahi, ne ya bayyana […]
Rundunar yan sandan jihar Kano, ta tabbatar da rasuwar mutane 5 yayin da wasu 10 suke samun kulawar likitotci a asibitin koyarwa na Mallam Aminu kano, biyo bayan tashin wani abun fashewa , a gidan Karfe dake kan titin Eastern Bypass. Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cewa da safiyar […]
Yayin da harkar Ilimi a Najeriya ke ci gaba da fuskantar matsaloli, wasu makarantun gwamanati a jihar Kano sun koka kan halin da makarantunsu ke ciki. Wanna na zuwa ne yayin da wata makarantar Sakandare dake karamar hukumar Tarauni , ta bayyana fargabarta game da makomar karatun yara, sakamakon zargin da ake yiwa wasu batagarin […]
Mai Martaba Sarkin Kano na 14m Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu ya bayyana takaicinsa yadda ake fama da fadan daba da shan miyagun kwayoyi da sace-sacen wayoyin da suka zama ruwan dare a jihar nan. Sarkin ya bayyana hakan ne lokacin da yake samun korafe-korafen al’ummar a unguwannin Sheka da Maidile da Ja’oji da dai sauran […]
Rundunar ‘yansanda jihar Kano a Najeriya ta sanar da kama mutum 51 da take zargi da zama ‘yan daba a cikin wani samame da ta kwashe kwana uku tana kai wa a unguwanni daban-daban na na garuruwa cikin ƙwaryar birnin jihar. Ta kuma ce an samu makamai da miyagun ƙwayoyi daga hannun waɗanda ta kama […]
Rundunar Ƴan sandan jihar Kano ta lashi takobin kakkaɓe matsalar faɗan Daba, da fashin wayoyin jama’a da muggan makami, da Shaye-shayen kayan maye, da ke addabar jama’a jihar, don wanzar da zaman lafiya. Kwamishinan Yan Sandan jihar Kano,CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan ta cikin sanarwar da mukaddashin kakakin rundunar ƴan Sandan jihar […]
Masu ƙwacen waya sun kashe wani ma’aikacin Jami’ar Northwest da ke Kano, Buhari Imam, ta hanyar daɓa masa wuƙa a ciki.