Gwamnatin Kano Ta Yi Tir Da Kisan Matasa Biyu A Benue

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya yi kakkausar suka tare da yin Allah-wadarai da kisan gillar da aka yi wa wasu matasa biyu ‘yan jihar a garin Makurɗi, babban birnin jihar Benue.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce, a jiya Litinin ne da misalin ƙarfe 11:00 da dare wasu da ba a gano ko su waye ba har yanzu suka far ma matasan biyu – Barhama Suleiman da Jamilu Ahmad, inda suka yi musu kisan-gilla, haka kawai.

A sanarwar gwamnan ya bayyana harin a matsayin na dabbanci da rashin imani da hankali, wanda ba za a lamunta da shi ba.

A yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga ‘yan uwa da iyalan mamatan Abba Kabir ya jajanta wa fitaccen malamin nan na addinin Musulunci Sheikh Ibrahim Khalil wanda shi ne tamkar mahaifi a garesu.

Sannan ya roƙi jama’ar jihar ta Kano da su kwantar da hankalinsu, inda ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta yi duk abin da ya wajaba don ganin an yi bincike a kan lamarin tare da hukunta waɗanda suka yi kisan.

Wannan ya faru ne kuwa yayin da ake ci gaba da alhinin kisan-gillar da aka yi wa wasu ‘yan jihar Kaduna, 12 a garin Mangu na jihar Filato.

Post masu alaƙa

Ƙungiyar muhaɗu mugyara ta bayyana Muhasa TVR a matsayin kan gaba wajen gyaran tarbiyyar al’umma.

Fursuna ya tsere bayan hatsarin motar jami’ai a Yobe

Katsina ta kafa kotunan tafi da gidan ka don gaggauta hukunta ’yan ta’adda