Rundunar Ƴan sandan jihar Kano ta lashi takobin kakkaɓe matsalar faɗan Daba, da fashin wayoyin jama’a da muggan makami, da Shaye-shayen kayan maye, da ke addabar jama’a jihar, don wanzar da zaman lafiya.
Kwamishinan Yan Sandan jihar Kano,CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan ta cikin sanarwar da mukaddashin kakakin rundunar ƴan Sandan jihar Kano,DSP Abdullahi Hussaini ya Sanya wa Hannu a madadin kwamishinan.
Sanarwar ta ce, CP Bakori, ya ƙaddamar da sabbin matakan daƙile ayyukan ’yan daba da masu fashin waya da makami a birnin Kano da kewaye.
DSP Hussaini,ya kara da cewa kwamishinan ya gana da manyan jami’an rundunar ne a ranar Asabar 14 ga watan Yunin 2025, inda ya umarce su da su soma sumame a dukkan maɓoyar Ƴan Daba, tare da haɗin gwiwa da shugabannin al’umma domin ganin an cafko duk masu hannu a tashe-tashen hankula a faɗin jihar.
kwamishinan ya umarci dukkanin Baturen Ƴan Sanda wato DPO’s, da shugabannin shiyya na Ƴan Sanda, da sauran dakarun Ƴan sanda, da su nemi haɗin kai da al’umma, tare da ƙara faɗaɗa sintiri don magance matsalolin Daba, da fashin Waya a Kano.
Har ila yau, rundunar ƴan sandan ta kuma buƙaci haɗin kan jama’a da su rika bayar da bayanan sirri a kan yan daban, ta hanyar kiran waɗannan lambobin wayar 08032419752, ko 08123821575, 09029292926.