Donald Trump Ya Gurfana a Gaban Kotu Bisa Zargin Aikata Wasu Laifuka
Ana zargin tsohon shugaban ne da biyan wata jarumar fina-finan batsa, Stormy Daniels toshiyar baki don ka da ta yi bayani game da alaƙar da ta taɓa shiga tsakaninsu lokacin da yake takarar shugabancin ƙasar a zaben 2016.










