Nigeria

Muna Buƙatar Masu Fassara A Asibitoci : Kurame

Al’ummar kurame sun koka bisa matsalolin da suke fuskanta a fannin kiwon lafiya, sakamakon rashin masu yi musu fassara a asibitoci a Jihar Yobe. Malam Kolo Abba, Shugaban Ƙungiyar Kurame a Ƙaramar Hukumar Damaturu, ya ce kurame majinyatan sukan koƙarta wajen fahimtar ƙa’idojin likitoci da na kiwon lafiya, amma duk da hakan suna cikin haɗari. […]

Read more

ASUU Na Barazanar Shiga Yajin Aiki A Jami’o’in Najeriya

Ƙungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta bayyana cewa dukkan jami’o’in gwamnati kusan 150 da ke ƙarƙashin kulawar ta na iya shiga yajin aiki, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito. Wannan lamari ya biyo bayan da gwamnati ta musanta cewa ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da ASUU, inda ta bayyana takardun da ƙungiyar […]

Read more

An Kashe Mutane 3 A Faɗan Kungiyoyin Asiri A Legas

Aƙalla mutum uku ne sun rasu, yayin da wani ɗan sanda ya ji rauni a wani rikicin ƙungiyoyin asiri da ya auku a kasuwar Owode Onirin da ke Jihar Legas. Rundunar ’yan sandan jihar, ta bayyana cewa tana neman Abiodun Ariori, Shugaban Kamfanin Golden Venture Limited, bisa zarginsa da hannu a rikicin. Shaidu sun ce […]

Read more

Tinubu Ya Gana Da Shugaban Brazil Lula

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gana da takwaransa na Brazil, Luiz Inacio Lula da Sailva a birnin Brasilia bayan shugaban na Najeriya ya isa ƙasar. Shugabannin biyu za su tattauna inganta haɗakar diflomasiyya da sauran abubuwan da suka ce zai amfani ƙasashen biyu. A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya Bayo Onanuga […]

Read more