Yadda Hatsarin Jiragen Ruwa Ya Ci Rayuka 108 A Sakkwato

Hatsarin jiragen ruwa ya ci rayuka akalla 108 a Jihar Sakkwato a cikin shekaru biyar da suka gabata.

Mutane da dama sun bace a sakamakon hatsarin jiragen ruwan da aka samu akalla sau takwas a jihar a daga shekarar 2020 zuwa yanzu.

Bincikenmu ya gano cewa daga shekarar 2020 zuwa 2025 an rasa rayuka akalla 1,600 a sanadiyyar hatsarin jiragen ruwa a sassa daban na Najeriya.

Na baya-bayan nan shi ne wanda ya auku a ranar Lahadi, inda jirgin ruwa dauke da fasinjoji 51, inda aka yi nasarar ceto mutum 26, wasu 25 ake ci gaba da neman su a yankin Karamar Hukumar Goronyo da ke Jihar Sakkwato.

Nigeria na da albarkatu masu yawa, ciki har da hanyoyin ruwa da ke yawo a jihohi 28, suna da tsawon fiye da kilomita 10,000. Hukumar Kula da Hanyoyin Ruwa ta Kasa (NIWA) ta bayyana cewa kimanin kilomita 3,800 daga cikin wadannan hanyoyin ruwa ana safara da su wajen safarar kaya da fasinjoji.

Sai dai duk da wadannan albarkatu, Najeriya na ci gaba da fuskantar asarar rayuka a hanyoyin ruwa sakamakon rashin tsauraran dokoki da kuma rashin bin ka’idojin tsaro.

Binciken Hukumar Binciken Hadurra ta Najeriya (NSIB) ya nuna cewa fiye da rabin mutanen da suka mutu a hadurran jirgin ruwa sun mutu ne ta hanyar nutsewa, kashi 90% daga cikinsu ba su sanya rigar kare rai ba .

A Arewacin Najeriya, inda ake ci gaba da amfani da kwalekwalen gargajiya a matsayin hanyar sufuri, daruruwan mutane sun rasa rayukansu a cikin shekaru.

 

Post masu alaƙa

Ƙungiyar muhaɗu mugyara ta bayyana Muhasa TVR a matsayin kan gaba wajen gyaran tarbiyyar al’umma.

Fursuna ya tsere bayan hatsarin motar jami’ai a Yobe

Katsina ta kafa kotunan tafi da gidan ka don gaggauta hukunta ’yan ta’adda