Babu Wasu Masu Adawar Da Za Hana Tinubu Cin Zaɓen 2027 — Ganduje
Tsohon gwamnan jihar kano kuma shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya ce babu wata gamayyar ’yan adawa da za ta iya hana Shugaba Bola Ahmed Tinubu lashe wa’adi na biyu a zaɓen 2027 idan Allah ya kai mu.









