Tashar Tsandauri Ta Dala Inland Dry Port Ta Magantu Kan Cece-Kucen Korar Ma’aikata.

Tashar tsandauri ta Dala Inland Dry Port dake jihar Kano, ta barranta kanta daga cece-kucen da ake ci gaba yi kan rashin biyan wasu tsoffin ma’aikatan ta hakkokinsu.

Mai mataimakawa shugaban tashar Tsandaurin ta Dala Inland Dry Port, Dr. Kabir Abdul’aziz, shi ne ya musanta zargin da cewa wasu ne kawai suke amfani da tsoffin ma’aikatan don sanya siyasa, amma dukkan ma’aikatan da suka gama aiki da tashar an biya su hakkokinsu.

Haka zalika ya kara da cewa su rage ma’aikata suka yi maimaikon kora da wasu ke yadawa cewar an kore su ne saboda su yan asalin jihar Kano ne.

Sai dai Dr. Kabir ya ce  ba iya yan jihar Kano lamarin ya shafa ba, kuma a yanzu wadanda suke aiki a wajen yan jihar Kano, sunfi na sauran jahohi yawa.

‘’ a cikin mutane 61 da suke aiki a yanzu haka yan asalin jihar Kano 57 ne suke aiki a wajen yayin da sauran mutane 4 kawai yan sauran jahohi’’.

Sannan ya ce kowa yana so a dauke aiki amma babu wanda yake so a sallame shi , kawai bita da kulli ake yi musu saboda an sallami wasu daga aiki , amma ba dan ana so ba aka yi ba yanayi ne na harkokin kasuwanci ya kawo haka da kuma sauye-sauye da aka ci samu na koma baya.

Ya kuma musanta zargin rashin biyansu fanso bayan sun kammala aiki.

‘’ sha’ani na kasuwanci yau kai ne ka dauki mutane 10 da ana kasuwancin nan sai yanayin ya chanja dole kaima sai duba kaga cewa ya za a wajen daidaita al’amura’’.

A kwanakin baya ne wasu tsoffin ma’aikata suka fito tare da bayyana cewa tashar bata biya su hakkokinsu bayan sun bar aiki da kuma zargin an kore su saboda su yan Kano ne.

A karshe ya ce suna da cikkakun hujjojin biyan tsoffin ma’aikatan daga farko zuwa yanzu tun daga ranar da suka fara aiki.

Related posts

NOA Ta Rushe Rundunar Yaki Da Rashin Da’a Ta War Against Indiscipline(WaI) Brigade

Masu Kwacen Waya Sun Kashe Ma’aikaciyar Lafiya A Zariya

Gwamnan Kaduna Uba Sani Ya Yi Wa Ma’aikatan Manyan Makarantu Karin Kashi 70 A albashi