Dole A Janye Jami’an Yan Sanda Daga Gadin Manyan Mutane – Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya nanata ƙudurinsa na janye ƴansanda daga gadin manyan mutane a ƙasar, inda ya ce janyewar ta zama tilas.

Ya ce babu gudu babu ja da baya a matakin da ya ɗauka, sannan ya yi kira ga dukkan ministocin ƙasar su yi abin da ya dace ba tare da ɓata lokaci ba.

Tinubu ya bayyana haka ne a taron majalisar zantarwa na ƙasar, inda ya yi gargaɗin ɗaukar mataki kan waɗanda suka saɓa umarnin.

“Idan dole kana buƙatar ƴansanda saboda yanayin aikinka, sai ka yi magana da babban sufeto janar na ƴansa, sai a nema sahalewa ta,” in ji shi.

Shugaban ya buƙaci mai ba shi shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu da ministan ƴansanda Ibrahim Geidam da shugaban ƴansanda Kayode Egebtokun su tabbatar an aiwatar da umarnin.

Tinubu ya ce kariya ga manyan mutane ba aikin ƴansanda ba ne, inda ya ce ministan harkokin cikin gida Olobunmi Tuni-Ojo zai yi tsare-tsaren maye gurbin ƴansanda da suke aiki da manyan mutane a ƙasar da jami’an tsaron civil defence, waɗanda an horar domin “ba manyan mutane kariya, kuma suna ɗaukar bindiga.”

Post masu alaƙa

Hukumomin tsaro sun kama wanda ya kirkiri hukumar bogi a Nijeriya

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama dan bindiga da sanye da kayan sojoji.

Majalisar Wakilai ta janye kudirinta kan ‘yan sandan jihohi tare da yin nazari kan buƙatar Tinubu