Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC na ci gaba da tsare tsohon ministan shari’a kuma tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami (SAN), saboda zarginsa da hannu wajen tallafa wa ayyukan ta’addanci a ƙasar.
Binciken ya kuma shafi zuba jarin da ake zargin ya kai kusan naira biliyan 10 a Jihar Kebbi, da kuma batun dawo da dala miliyan 322 na kudaden Abacha daga Switzerland, da ƙarin dala miliyan 22 daga tsibirin Jersey.
Hukumar ta ce tana buƙatar cikakken bayani game da waɗannan al’amura kafin ta sake shi daga tsarewa.
EFCC ta ci gaba da tsare Malami har zuwa ƙarfe 10 na daren Talata saboda rashin cika sharuddan belinsa.
Ana binciken zargin amfani da asusun da ake zargin an ƙirƙire su ne domin karkatar da kuɗi, tare da yiwuwar ƙwace wasu kadarorinsa idan hujjoji sun tabbata.
Sai dai a nasa bangaren, Malami ya karyata duk tuhume-tuhume, yana jaddada cewa a lokacin da yake minista, shi ne ma ya jagoranci tsare-tsare da suka taimaka wajen cire Najeriya daga jerin ƙasashen da ake zargi da taimaka wa halatta kudaden haram.
A cikin sakon da ya wallafa a shafin X, ya ce ba a taɓa zarginsa ko gayyatarsa ko bincikar shi kan batun daukar nauyin ta’addanci ba, a Najeriya ko a waje.
Tsohon ɗan majalisar jihar Kebbi kuma na kusa da Malami, Abubakar B. Sabo, ya ce ba su ga dalilin da zai sa a alakanta shi da ta’addanci ba.
A cewarsa: “Ai kowa ya san cewa mutum da ya rike mukamin ministan shari’a na ƙasa ba zai iya zamewa wanda ke ɗaukar nauyin ta’addanci ba; kawai bita da kulli ake masa.”
Ya kuma kara da cewa: “Tunda an ce yana da hannu, muna jira mu ga ko za a iya tabbatar da hakan. Amma abin da ya dace shi ne a yi masa shari’a, ba kawai a kama shi ba tare da hujja ba.”
Ana sa ran Malami zai ci gaba da kasancewa a hannun EFCC har sai ya kammala cika dukkan sharuddan belinsa, tare da bayar da bayanan da masu bincike ke bukata.