Home » Tinubu Ya Cire Mele Kyari Daga Shugabancin NNPCL

Tinubu Ya Cire Mele Kyari Daga Shugabancin NNPCL

by Mujahid Wada Guringawa
0 comment

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya sauke Mele Kyari daga shugabancin kamfanin mai na ƙasar NNPCL a wani mataki na yin gagarumin garambawul ga kamfanin.

Wata sanarwa da Bayo Onanuna, mai magana da yawun Shugaba Tinubu ya fitar ranar Laraba ta ce an naɗa Bashir Bayo Ojulari a matsayin sabon shugaban NNPC.

Tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ne ya naɗa Mele Kyari a matsayin shugaban kamfanin mai na ƙasar NNPC a shekarar 2019 bayan Maikanti Baru ya yi ritaya.

Sanarwar ta ƙara da cewa Shugaba Tinubu ya yi garambawul ga kwamitin gudanarwar NNPC mai mutum 11 ƙarƙashin jagorancin Cif Pius Akinyelure wanda aka naɗa a watan Nuwamba na shekarar 2023.

An naɗa sabbin mambobin kwamitin gudanarwar NNPC wanda Ahmadu Musa Kida zai jagoranta.

Shugaba Tinubu yana sa rai sabon kwamitin gudanarwar ya ƙara adadin ɗanyen man da NNPC yake tacewa zuwa ganga 200,000 nan da shekarar 2027 sannan ya kai ganga 500,000 zuwa shekarar 2030, in ji sanarwar.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?