Home » Tinubu Ya Lashi Takobi Sai An Ƙara Haraji A Najeriya

Tinubu Ya Lashi Takobi Sai An Ƙara Haraji A Najeriya

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi watsi da shawarar Majalisar Tattalin Arziki (NEC) wadda ta nemi ya janye ƙudirinsa na ƙara haraji.

Wannan na zuwa ne duk da adawar da Ƙungiyar Gwamnonin Arewa ta bayyana dangane ƙudirin.

Ƙungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya da ke wakiltar jihohi 19 ta ce ƙudurin na shugaba Tinubu ya saɓa wa muradun jama’ar Arewacin ƙasar.

Majalisar Tattalin Arziki (NEC) ta soki ƙudurin a zaman da ta gudanar a ranar Alhamis.

NEC ta ba shawarar neman a jingine ƙudirin ƙara haraji, ta ce a yi wani abu da zai buɗe ƙofar tuntuɓar dukkanin masu ruwa da tsaki, kafin a yanke hukunci.

Bayan wannan shawara ta NEC ce dai wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya fitar a ranar Juma’a ta bayyana cewa shugaba Tinubu ya buƙaci NEC da ta bari a aiwatar da sabuwar dokar ƙarin haraji a Najeriya.

Sanarwar ta yaba wa Majalisar Tattalin Arzikin Najeriya dangane da shawarar da ta bayar.

Kazalika sanarwar ta tunatar da majalisar tattalin arzikin Najeriya muhimmancin ƙara harajin domin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar.

 

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?