Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sake sanya ranar 21 ga watan Augustan 2025, don sake gudanar da zaben cike gurbi na dan majalissar jiha, a kwatinan zabe guda biyar da bai kammalu ba, a karamar hukumar Kaura Namoda dake jihar Zamfara.
Kwamishinan zaben jihar, Dakta Mahmud Isah, ne ya bayyana hakan yayin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar, a ranar talatar data gabata.
Isah , ya bayyana cewa zaben cike gurbi na ranar 16 ga watan augusta 2025 da aka gudanar bai kammalu ba , sakamakon matsalolin da aka fusknata shi yasa aka sake soke wasu rumfunan zabe.
A cewarsa, za a gudanar da zaben a rumfuna uku dake Kyambarawa Shiyar Magaji (Kofar Hamza) 002 da Tukasu (Sabuwar Kasuwa) 009, da Kofar Fafa (Shiyar Fada).
- Yadda Hatsarin Jiragen Ruwa Ya Ci Rayuka 108 A Sakkwato
- Rundunar Yan Sandan Kano Za Ta Ladabtar Da Wasu Jami’anta Da Aka Gani A Bidiyon Karbar Kudi
Haka kuma, za a yi zaɓen a rumfunan zaɓe biyu da ke gundumar Sakajiki—Alko (Shiyar Kudu) 002 da Shiyar Nufawa (Kofar MD Nuhu) 007.
Jami’in tattara sakamakon zaben, Farfesa Lawal Sa’adu daga Jami’ar Tarayya da ke Gusau, ya bayyana cewa mutane 5,446 aka yi wa rajista a wuraren da abin ya shafa, kuma mutane 3,265 ne suka karɓi katin PVC, amma sakamakon da zaben ya nuna cewar jam’iyyar APC ta samu ƙuri’u 7,001, yayin da jam’iyyar PDP ta samu ƙuri’u 5,339,” in ji Sa’adu.
Hakan ta sanya aka soke zaben wuraren da lamarin ya shafa, saboda samun kuri’u sama da wadanda suka karbi katinan zabensu