Wasu ’yan bindiga sun harbe malamin Jami’ar Nnamdi Azikiwe (UNIZIK), Dokta Osita Chinedu, har lahira a daren Litinin a Jihar Anambra.
Wadan da abin ya faru a gabansu sun bayyana cewa ’yan bindigar sun tsayar da motar malamin, kafin suka harbe shi kuma suka tsere da motarsa ƙirar Toyota Corolla.
- Malam Uba Sani Ya Mayarwa Iyalan Abacha Filayen Da El Rufai Ya Karbe
- Hukumar Rawa Ta Najeriya Za Ta Kaddamar Da Kirkirarriyar Fasahar Zamanin Kallon Al’adu
Kawo yanzu Rundunar ’yan sandan Jihar Anambra, ta tabbatar da lamarin, tare da bayyana cewa ta fara bincike domin gano wadan da suka aikata mummunan aikin.
’Yan sanda sun buƙaci duk wanda ke da bayanan da za su taimaka wajen kama masu laifin ya kai rahoto zuwa ofishin ’yan sanda mafi kusa da shi.