Rundunar yan sandan jihar Kano ta fara gudanar da bincike kan wani mummunan kisan gilla da aka yi wa wata mata da yayanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi da ke cikin birnin Kano.
Kakakin rundunar yan sandan jihar CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce sun samu kiran gaggawa da misalin karfe 12:10 na rana, inda aka sanar da su cewa wasu da ba a san ko su waye ba sun shiga gidan Haruna Bashir.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa matar, Fatima Abubakar mai shekaru 35 da ’ya’yanta shida, sun samu munanan raunuka bayan da batagarin suka shiga gidansu tare da amfani da muggan makamai akan su.
Bayan samun rahoton, kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya umarci wata tawaga ta musamman karkashin jagorancin mukaddashin kwamishinan yan sanda mai kula da ayyuka, DCP Lawal Isah Mani, da su gaggauta zuwa wajen da abin ya faru.
Sanarwar ta ce tuni an kwashi gawarwakin wadanda abin ya shafa zuwa kwararru na Asibitin Murtala Mohammed dake Kano, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsu.
Wadanda aka yi wa kisan gillar sun hada da matar aure Fatima Abubakar da yayan ta, Maimuna Haruna mai shekaru 17 da Aisha Haruna mai shekaru 16 da Bashir Haruna mai shekaru da Abubakar Haruna mai shekaru 10 da Faruk Haruna mai shekaru 7 da Abdussalam Haruna mai shekara 1 da rabi.
Hakazalika, kwamishinan yan sandan ya ba wa sashin binciken manyan laifukan sirri na CID, karkashin jagorancin ACP Wada Jarma, umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da gurfanar da su a gaban shari’a.
Rundunar ’Yan Sandan ta kuma mika sakon ta’aziyya ga iyalan mamatan, da al’ummar Dorayi Chiranchi, da kuma daukacin al’ummar Jihar Kano.