Yan Sanda Sun Gurfanar Da Wanda Ake Zargi Da Satar Sarkar Karfe

 

Rundunar yan sandan jihar Oyo, ta gurfanar da wani mutum mai suna , Michael Jeremiah, a gaban kotun magistiri Iyaganku, dake Ibadan bisa zarginsa da satar sarkar karfe mai kimar kudi naira dubu dari biyu N200,000.

Mai gabatar da kara ya karantawa Jeremiah kunshin tuhumar sata inda nan take ya musanta zargin.

Sai dai mai gabatar da karar , Insifekta Olalekan Adegbite, ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 25 ga watan Mayu 2025, a yankin Odo-Ona Kekere a Ibadan babbar birnin jihar Oyo.

 

Ya kara da cewa Sarkar da ake zargin ya sace mallakar wani mai suna ,Mr. Peter Alfred , kuma laifin da ya aikata ya saba da sashi na 390 tara cikin baka ( 9)  na kundin dokokin laifuka na jihar Oyo shekarar 2,000.

Alkaliyar kotun mai shari’a , Mrs. Kausarat Ayofe, ta sanya shi a hannun beli bisa sharadin ajiye naira dubu hamsin 50,000 da kuma mutum daya da zai tsaya masa, sannan ta dage ci gaban shari’ar zuwa ranar 15 ga watan Yuli 2025.

Post masu alaƙa

An kama mutum 2 a hanyar kai wa ’yan ta’adda harsasai 314

Hukumomi a Nijar sun nemi ƴan ƙasar su yi wa jami’an tsaro uziri

Yadda magoya bayan Obi da Kwankwaso suka kafa ƙungiya don samun tikitin ADC