Yan Sanda Sun Kaddamar Da Operation Kukan Kura Tare Da Kama Mutane 98 A Kano

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta kaddamar da Operation Kukan Kura, don ci gaba da yaki masu aikata laifuka a fadin jihar, tare da kama wadanda ake zargi da aikata laifuka mabambanta su 98 tare da kwato kayayyaki daga wajensu.

Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana a taron manema labarai da aka gudanar, a shelkwatar rundunar dake unguwar bompai.

CP Bakori, ya ce bisa dabarun da rundunar yan sandan ta dauka wajen yaki da laifuka , an samu nasarori sosai wajen dakile dukkan nau’ikan laifuka a fadin jihar Kano.

A cewarsa sun gudanar da wani nazari da bincike na musamman akan halin da tsaron jihar ke ciki, shi yasa suka kaddamar da tsarin mai taken Operation Kukan Kura tare da yin aiki da al’umma wajen basu hadin kai da kuma bayanan sirrin da zai hana aikata laifuka.

Kwamishinan ya kara da cewa manufar shirin, shi ne yin amfani da fasaha da badaru wajen ganowa da kuma hana faruwar laifuka, kamar fadan daba, fashi da makami, a cikin birnin Kano, harma da hana fataucin miyagun kwayoyi.

Rundunar ta ce bayan ta kaddmar da shirin, a ranar 1 ga watan Yuli 2025, an samu nasara sosai, bayar taron manema labarai data gudanar a ranar 16 ga watan Yuni 2025 , kwanaki 24 da suka gabata zuwa yanzu sun kama mutane 98 da ake zargi da iakata manayan laifuka 21, wadanda suka hada da fashi da makami, Daba, fataucin miyagun kwayoyi, sata, zamba da dai sauransu.

Wasu daga cikin abubuwan da aka kwato sun hada da , Muggan Makamai, Motoci guda 6 , Adaidaita Sahu guda 8 babura 10, Sholisho guda 42,Sinƙin Tabar wiwi (cannabis sativa) guda 35, kullin wiwi guda 1,123, Madarar sukudayin Kwalba 86, Kwayar Exol Sacet 30, yar ɗiba guda 43, Kwayar Diazepam Sachet 10 , yar diba guda 53, Adduna guda 16, Wukake guda 98, Kudin jabu Dalar Amurka $10,000, Wayoyin hannu guda 13, Batirin mota guda 5, Tayar mota guda 3.

Haka zalika an kama mutane garkuwa da mutane 4, yan fashi da makami 21, masu fataucin miyagun kwayoyi 5, Barayin motoci 12, masu zambatar mutane 4 , yan daba 47 sai kuma barayi mutum 5.

Kwamishinan ya kara da cewa wannan sabon aiki na ‘Operation Kukan Kura’ ana yinsa tare da wasu dabarun aiki na musamman wanda ya hada da tattara bayanan sirri da  farmakar maboyar ɓata gari tare da hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da  tattaunawa da shugabannin gargajiya, shugabannin addini, kungiyoyin matasa, Kungiyoyi masu zaman kan su, da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da tsaro mai dorewa.

A karshe rundunar ta sake jinjinawa jama’ar jihar Kano bisa hadin kai da goyon baya da suke ba rundunar ‘yan sandan.

 

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda