Yan Sanda Sun Kama Kwaya Ta Sama Da N40m Tare Da Cafke Gawurtattun Yan Fashi A Kano

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta bankaɗo wasu miyagun ƙwayoyi, da darajar kudin su ta kai sama da Naira miliyan 42, tare da cafke wasu fitattun mutane da ake zargi da aikata laifin fashi da makami.

Wannan na cikin sanarwar da kakakin rundunar ƴan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce, a wani samame da aka gudanar, jami’an rundunar sun cafke, Nura Sani mai shekara 20 dan jihar Bauchi da kuma Ibrahim Lawan mai shekara 35 dan jihar Katsina, bisa zargin yin fashi ayankin Tokarawa Quarters ranar 14 ga Satumbar daya gabata.

An yi zargin cewar sun ƙwace motar Mercedes Benz GLK mai darajar Naira miliyan 26.5m da wayoyi da sauran kayayyaki.

Haka kuma, a Jalli dake karamar hukumar Dawakin Tofa, an gano fakiti 540 na maganin Pregabalin da darajarsu ta kai naira miliyan 40.5m.

Haka zalika a ranar 30 ga Satumba 2025 an kama wani mai suna Alhaji Isyaku Babayo  Kofar Mazugal da Mohammed Ahmed Dorayi Babba a unguwar  Trailer Park, Dangauro, dauke da jakunkuna 7 na ruwan maye “Akuskura” jimilla kwalabe 2,450.

Yanzu haka dai rundunar ta  miƙa miyagun kwayoyin ga hukumar NDLEA, domin ci gaba da bincike kafin a gurfanar da su a gaban kotu don su fuskanci hukunci.

Post masu alaƙa

2027: Tinubu da Atiku da Obi za su fafata a muhawarar ƴan takarar shugaban ƙasa

2027: NDC ta zargi APC da gwamnatin Kano da shirin yin magudi ta tsarin tattara sakamakon zabe na INEC

Yan sanda sun buƙaci haɗin kan al’umma wajen yaƙi da shaye-shayen miyagun kwayoyi a Kano