Babu Inda Na Ce Zan Janye Wa Wani Takarata – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya musanta rahotannin da ke cewa zai janye wa wani takararsa a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.

Wannan na zuwa ne bayan wata hira da Atiku yayi da BBC Hausa a ranar Laraba, 1 ga watan Oktoban 2025, ranar da Najeriya ke bikin cika shekara 65 da samun ƴancin kai kenan.

A cikin wata sanarwa da mai bai wa Atiku shawara da yaɗa labarai, Paul Ibe ya fitar, ya ce “An sami ruɗani daga wasu kafafen yaɗa labarai kan fassarar hirar da Atiku ya yi da BBC Hausa.”

“Ya ce bayan an yi nazari kan bidiyo da rubutaccen hirar, babu inda ya ce zai janye wa kowa takararsa.

Sanarwar ta kara da cewa abin da Atiku ya bayyana a fili shi ne matasa da sauran masu sha’awar takara suna da damar shiga zaɓen fitar da gwani.

Ya kuma ce “Idan matashi ya fito ya ci nasara a zaɓen fitar da gwani, shi zai goyi bayan wannan ɗan takaran ba tare da wata matsala ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa duk wani jita-jita da ke cewa Atiku zai janye daga takara don wani ba gaskiya ba ne, kuma bai yi daidai da abin da ya faɗa a hirar da ya yi da BBC Hausa ba.

Post masu alaƙa

Ba za mu buɗe Hormuz ba sai Amurka ta buɗe tashar ruwanmu – Iran

Jirgin ‘yan cirani ya kife a tekun Libiya

Da buƙatar samar da takin zamani ga manoman Najeriya – MDD