Yan Sanda Sun Kama Mutanen Da Ake Zargi Da Lalata Taransifoma A Hadejia

Rundunar yan sandan jihar Jigawa, ta samu nasarar kama wasu mutane da ake zargi lalata Taransifoma, a karamar hukumar Hadejia.

Kakakin rundunar yan sandan jihar SP Shisu Lawan Adamu, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

Sanarwar ta ce an kama batagarin lokacin da suke barnata na’urar wutar lantakin, wadanda suka fito daga jahohin Kano, Bauchi da kuma Jigawa.

Haka zalika ana zargin sun kware wajen lalata taransifoma tare da siyar da ita a garuruwa dabanm-daban.

Wadanda ake zargin sun hada sun hada Haruna Musa dan shekaru 36 , Hussaini Innocent, Abubakar Yakubu , Zakariyya Mohammed, Mamman Danladi , Khalifa Yahaya, Ibrahim Mohammed,  Ali Ibrahim.

Hakazalika, an kara kama wasu matasan a garin Bamaina a lokacin da suke kona wayar wutan lartarki a wata makaranta wadda kudin wayar yakai naira miliyan bakwai (7).

SP Shisu Adamu, ya kara da cewa tuni sun gurfanar da wasu daga cikin matasan, a gaban kotu, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike don kamo sauran da suka gudu da kuma masu siyan kayan satar.

Post masu alaƙa

Nafi’u ya gargaɗi Atiku ya daina sukar Tinubu da sunan ADC

Yan Sandan a Kano sun kama mutane 244, ciki har da 117 da ake zargi da fadan daba.

Ƴansanda sun ƙara tsaurara matakan tsaro a bikin Takutaha, tare da gargaɗin masu yunkurin tada zaune tsaye.