Kungiyar Lauyoyi Ta Bukaci Mambobinta Su Yi Taka Tsan-tsan Wajen Yin Amafani Da Fasahar AI

Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya NBA, ta buƙaci mambobinta da su yi taka tsan-tsan wajen amfani da sabuwar fasahar AI wajen samun bayanai domin inganta aiyukansu.

Shugaban kungiyar reshen Jihar Kano shiyar Karamar hukumar Ungoggo, Barista Ahmad Abubakar Gwadabe, ne ya bayyana hakan, yayin wani taron wuni guda da kungiyar ta shirya don ilimintar da mambobinta kan dokar da ta ke bayani kan masu amfani da rubutu da hotuna da wani ya wallafa a yanar gizo.

Da yake jawabi ya yin taron shugaban kungiyar na jihar kano reshen ungoggo, Barista Ahmad Abubakar, ya ce taron zai taimakawa lauyoyin sanin hukunce-hukuncen dokar dake yaki da masu satarwa mutane bayanai da hotuna da kuma bidiyon da suke wallafawa a yanar gizo.

Anasa bangaren, shugaban hukumar kare bayanai na shiyar jihar Kano da Katsina, Sani Ahmad, ya bayyana cewa wannan taron muhimmin abune ga lauyoyi da ma sauran al’umma.

Farfesa Kabiru Adamu malami a bangaren shari’a dake jami’ar Bayero Kano, ya bayyana cewa, taron zai wayarwa da sauran mutane kai wajen kare bayanansu na yanar gizo.

Taron dai ya zo ne, adai-dai lokacin da ake yawan samun yawaitar sace-sacen bayanan mutane da hotuna ta internet, wanda hakan ke janyowa mutane asarar makudan kudade.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda