Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Daddatsa Mahaifinsa A Jigawa

Rundunar yan sandan jihar Jigawa ta bayyana  cewa yanzu haka tana tsare da wani matashi bisa zarginsa da daddatsa mahaifinsa da Adda, wandada hakan ya yi sanadiyar rasuwarsa.

Kakakin ruazndunar yan sandan jihar , SP Shiisu Lawan Adamu , ne ya tabbatar da hakan a wani takaitaccen sako da ya aike wa da MUHASA TVR.

Sanarwar ta ce matashin da ake zargi yana da shekaru 20, amma rundunar bata bayyana sunansa ba ko kuma garin da ya fito.

SP Shisu Lawan ya tabbatar da cewa sun fara gudanar da bincike akansa kuma za su yi wa al’umma Karin haske anan gaba kadan.

Post masu alaƙa

JIGAWA: ‘Yan siyasa sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya gabanin zaben 2027

Sarkin Gumel Ahmed Muhammad Sani II ya rasu

Yan sanda sun kama mutane 79 tare da kwato kwayoyi da makamai a bikin Takutaha a Kano.