Yan Sandan Kano Sun Kama Wadanda Ake Zargi Da Fashin Babura A Medile Da Guringawa.

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta kama wani matashi mai suna, Sadik Idris da ake kira da Danhasa, mazaunin unguwar Medile, bisa zarginsa da haura gidajen mutane da makami suna yi mu su fashin Babura da wayoyi da sauran kayayyakin da suka mallaka.

Mai Magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa sun samu korafe-korafe daga unguwar Medile da kuma Garin Guringawa dake karamar hukumar Kumbotso, cewa wasu batagari suna tsallaka musu gidaje cikin dare, suna yi musu kwacen ababen hawa da wayoyi, kuma bayan samun korafin ne kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya tayar da dakarun yan sanda tare da basu umarnin kamo wadanda ake zargin.

CSP Abdullahi Kiyawa, ya kara da cewa tun a watan Nuwamba 2025 suka fara gudanar da bincike , kuma daman tuni sun kama mutane hudu da suka hada da Ibrahim Hamza, Bahari Usman, Shu’aibu Hamza da kuma Abdussalam Inusa wadanda aka gurfanar da su a gaban kotu kan wadannan manyan laifuka na fashi da makami .

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta ce tun daga wancan lokaci take farautar jagoran tawagar batagarin wato, Sadik Idris Danhansa, kuma yana wajensu yanzu haka haka don fadada bincike kafin gurfanar dashi a gaban kotu.

Post masu alaƙa

Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad Ya ce suna nema Jam’iyyar da za su shiga amma banda APC

Ƴan bindiga sun sace basarake da matarsa a jihar Kwara

Tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya Galadima ya rasu