Zan mayar da tallafin man fetur idan na ci zaɓe – Atiku

Ɗan takarar shugabancin Najeriya na babbar jam’iyyar hamayya ta ADC a zaɓen ƙasar mai zuwa, Atiku Abubakar ya yi alƙawarin cewa zai mayar da tallafin man fetur a ƙasar idan ya hau kan mulki a shekarar ta 2027.

Cire tallafin man fetur na daga cikin manyan matakan da gwamnatin Bola Tinubu ta ɗauka waɗanda suka kawo gagarumin sauyi a tattalin arziƙin ƙasar.

A ranar 29 ga watan Mayun 2023, Tinubu ya sanar a cikin jawabinsa na karɓar mulki cewa “tallafi ya ƙare”, lamarin da ya taka rawa wajen tashin farashin litar man fetur da hauhawar farashi a kusan kowane fanni na ƙasar.

Sai dai an yi ta cece-ku-ce kan rashin ganin alfanun hakan bayan da aka samu ƙarin tsadar rayuwa a ƙasar.

A tattaunawar da ya yi da kafafen yaɗa labarai a jiya Laraba, Atiku ya ce cire tallafin bai yi amfani ba kasancewar “ba a ga abin da aka yi da kuɗin ba”.

“Ina kuɗin suke? Ya kamata a ce an yi amfani da su wajen maganin talauci da rashin zuwa makaranta, da sauran su”.

A lokacin da aka tambaye shi ko zai mayar da tallafin man fetur ɗin idan ya ci zaɓe a 2027, sai ya ce: “Zan mayar, kuma duk wani wanda ya saci kudin zai dawo da su”.

Gabanin babban zaɓen 2023, Atiku Abubakar ya taɓa yin alƙawarin cewa zai sayar da matatun man fetur na ƙasar

Post masu alaƙa

Gwamnonin da ke shirin murɗe zaɓen 2027 za su sha mamaki — Kwankwaso

Zan tabbatar matatun man Najeriya sun koma aiki – Tinubu

Majalisar dokokin Kano ta dakatar da shugabannin ƙananan hukumomi uku