Za A Gina Layin Dogo Mai Amfani Da Lantarki A Kano

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta samar da titin dogo domin sufurin jirgin ƙasa a ƙwaryar birnin Kano da ke arewacin ƙasar, wanda zai laƙume naira triliyan 1 da rabi, a kamar yadda shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar wakilai Abubakar Kabir Abubakar ya bayyana.

Jaridar DailyTrust ce ta ruwaito ɗan majalisar yana bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyin ƴan jarida a Kano, inda ya ce shirin zai magance matsalolin da ake fuskanta a ɓangaren sufuri a jihar.

“Duk wanda ya yi tafiya zuwa Turai ko Asiya zai ga irin waɗannan jiragen ƙasan kuma zai san muhimmancin su. Shirin zai matuƙar taimakawa tattalin arziƙin jihar idan an kammala.”

Ya kuma ce Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da muhimman abubuwan ci gaba a arewacin ƙasar, kama daga ababen more rayuwa, da fannin lafiya, da noma da ilimi da kuma tsaro, ba kamar yadda mutane da dama ke zargi ba na cewa Tinubu ya mayar da yankin saniyar ware.

Post masu alaƙa

2027: Tinubu da Atiku da Obi za su fafata a muhawarar ƴan takarar shugaban ƙasa

2027: NDC ta zargi APC da gwamnatin Kano da shirin yin magudi ta tsarin tattara sakamakon zabe na INEC

Yan sanda sun buƙaci haɗin kan al’umma wajen yaƙi da shaye-shayen miyagun kwayoyi a Kano