Kamfanin Dillancin Wutar lantarkin Najeriya (TCN) ya ce ɓarayi sun sake lalata layinta mai karfin Volt 132 (KV) da wayoyin karkashin kasa a Abuja.
Babbar Manaja mai Hulda da Jama’a a TCN, Mrs Ndidi Mbah ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a, in da ta ce, lamarin ya haifar da katsewar wutar lantarki a tsakiyar birnin tarayya Abujaeda kuma wasu unguwannin da ke kewaye.
Madam Mbah ta ce ɓarayin sun yi wannan ɗanyen aikin ne da sanyin safiyar ranar Juma’a.
Ta ce kebul ɗin da ke karkashin kasa mai karfin 132kv da aka lalata ne ke da alhakin jigilar wutar lantarki daga babbar madatsar wutar zuwa cikin garin Abuja.
Ta ce, ɓarnar da aka yi a yankin babban lambun shakatawa na Millennium Park ya shafi kaso 60 na yankin.
Madam Mbah ta ce an sace kebul ɗin da ya kai tsayin mita 40 da kuma wasu kayayyakin aikin da ke kwance a cikin ƙasa.
Ta ce yankunan da a halin yanzu ke cikin duhu sakamakon wannan satar sun haɗa da Maitama, da Wuse, da Jabi, da Life camp, da Asokoro, da Utako, da Mabushi da wani sashe na fadar shugaban ƙasa.
Ta ce, “Bayan tabbatar da abin da ya faru, injiniyoyin TCN sun bazama aikin gyaran ba ji ba gani.
“Muna roƙon ‘yan Najeriya su taimaka wajen sa ido kan kayayyakin mu, su kuma rika bada bayanan sirri idan sun ga za a saci ko lalata kayan mu”