Ɗalibar Jami’ar IBB Ta Faɗi Ta Rasu

Wata ɗalibar aji biyu a sashen nazarin ƙwayoyin halittu da sunadarai na Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBBU), Lapai da ke Jihar Neja ta riga mu gidan gaskiya.

Aminiya ta ruwaito cewa, Fatima Adamu Muhammad, ta rasu ne bayan ta yanke jiki ta faɗi a wani matsuguninta da ke wajen makarantar.

Rahotanni sun ce ta fara ƙorafin cewa ba ta jin daɗin jikinta da alamu na rashin lafiya, inda daga daga bisani ta yanke jiki ta faɗi.

Sai dai bayan an garzaya da ita asibitin gwamnati na Lapai, likitoci suka tabbatar da cewa rai ya yi mata halinsa.

Mahukunta sun tabbatar da rasuwar ɗalibar da aka bayyana a matsayin babban rashi ga iyalai, makusanta da al’ummar jami’ar.

Wata sanarwa da shugaban sashen yada labarai na jami’ar, Alhaji Baba Akote, ya fitar, ya bayyana cewa ɗalibar tana da nutsuwa sannan mai hazaƙa ce da ladabi ga malamanta da kuma faran-faran a cikin ’yan uwanta ɗalibai.

Post masu alaƙa

Barista Hamza Ɗantani ya jinjinawa CP Bakori da wasu kwamishinonin yan sanda biyu.

Rundunar yan sandan jihar Kano ta ceto fasinjoji 9 bayan musayar wuta da yan bindiga a hanyar Doguwa.

Jigawa ta kaddamar da tsare-tsaren bunƙasa kananan hukumomi 27 na shekaru biyar.