Kotun Ƙoli Ta Kori ƙarar Jihar Osun Kan Riƙe Kudin Kananan Hukumomi

Kotun Ƙolin Najeriya ta yi watsi da ƙarar da jihar Osun ta shigar da gwamantin tarayya game da riƙe kuɗaɗen wasu ƙananan hukumomi na jihar, kamar yadda kafofin yaɗa labarai suka ruwaito.

Alƙalan kotun shida cikin bakwai sun ce Kwamashinan Shari’a na Osun Oluwale Jimi-Bada ba shi da haƙƙi a shari’ance ya shigar da Ministan Shari’a Lateef Fagbemi a madadin ƙananan hukumomin Osun 30.

Kotun ta ce shugabannin ƙananan hukumomin da ka rantsar bayan sun ci zaɓe su ne ke da alhakin shigar da ƙarar ko kuma a shigar da su ƙara kai-tsaye.

Mai Shari’a Mohammed Idris wanda ya karanto hukuncin, ya ce gwamnatin tarayya ta yi kuskure wajen riƙe kudin ƙananan hukumomin yana mai cewa ya saɓa wa tsarin mulki.

Ta kuma nemi gwamnatin ta APC ta tabbatar ta aika muu kasonsu daga asusun haɗaka.

Post masu alaƙa

INEC ta kai wa CBN ajiyar muhimman kayan zaɓen Gwamnan Osun

Hisbah za ta fara farautar masu aikata baɗala a Kano

Rundunar yan sandan shiyya ta daya ta kama Mutane biyar kan zargin jabun magunguna da sojan Gona.