Kungiyar Malamai Ta NUT Ta Karrama Malam Umar Namadi Da Lambar Yabo Ta “Gwamna Mafi Ƙwazo

Kungiyar Malamai ta Najeriya, NUT, ta karrama Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, da lambar yabo ta “Gwamna Mafi Ƙwazo a Arewacin Najeriya” a bangaren ilimi, saboda manyan gyare-gyaren da gwamnati ta aiwatar a fannin.

Tawagar NUT daga jihohi 19 na Arewa, ƙarƙashin jagorancin Comrade Muhammad Hambali, ta kai ziyara Fadar Gwamnatin jihar da ke Dutse domin mika lambar yabon.Hambali ya bayyana cewa Gwamna Namadi ya nuna bajinta wajen aiwatar da sabon tsarin albashi da daukar karin malamai, da biyan albashi kan lokaci, wanda hakan ne ya bambanta Jigawa da sauran jihohi.

Ya ce Gwamna Namadi ya zama abin koyi ga sauran gwamnoni, don haka yana kira a gare su da su je Jigawa su koyi salon inganta ilimi.A nasa bangaren, Gwamna Namadi ya gode wa kungiyar, ya kuma miƙa lambar ga malamai, yana mai cewa su ne ginshikin nasarar ilimi a jihar.

Ya kuma jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da zuba jari a bangaren ilimi don kara inganta shi

Post masu alaƙa

Najeriya na buƙatar ƙarin dala biliyan 410 domin cimma burinta na sauyin makamashi zuwa shekarar 2060.

Shugaba Tinubu ya lissafa nasarorin da ya samu a ƙasa da shekaru huɗu

Pantami ya lashe zaben fid da gwani na ɗan takarar gwamnan PDP a Gombe