Wani mummunan hatsarin mota da ya faru a kan babban titin Calabar

Daliban Jami’ar Kuros Ribas uku da ma’aikaci daya sun rasu a wani mummunan hatsarin mota

Wani mummunan hatsarin mota da ya faru a kan babban titin Calabar zuwa Itu a jihar Kuros Ribas ya yi sanadiyar mutuwar daliban Jami’ar uku da kuma ma’aikacin jami’ar daya.

Hatsarin ya faru ne sa’ilin da wata motar bas kirar coaster da ke dauke da daliban ta yi karo da wata babbar motar daukar kaya (tirela), yayin da suke kan hanyar dawowa daga wani aikin hukuma a garin Uyo na jihar Akwa Ibom.

Hukumar jami’ar ta bayyana a ranar Asabar cewa dalibai 24, wadanda akasarinsu mambobin kungiyar dalibai (SUG) ne, hatsarin ya ritsa da su a daren ranar Juma’a a yankin karamar hukumar Odukpani, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na jami’ar, Onen Ebri Onen ya fitar, makarantar ta tabbatar da rasuwar.

Post masu alaƙa

Ana zargin mahaifi da kashe ’yarsa kan auren dole a Katsina

An kama mutum 2 kan zargin sayar da filayen gwamnatin a Kano

Yadda wata tifa ta take mutum 2 a kan babur a Jos