• Home  
  • An Dauki Matakin Ba Sani Ba Sabo Kan Komawa Makarantu A Kano 
- Babban Labari - Labarai

An Dauki Matakin Ba Sani Ba Sabo Kan Komawa Makarantu A Kano 

Kwamishinan  Ma’aikatar Ilimi ta jihar Kano Dakta Ali Haruna Makoda, ya kai ziyar bazata makarantar sakandare ta maza dake yankin Gano a Karamar hukuma dawakin kudu.

Aliyu Wali

Kwamishinan  Ma’aikatar Ilimi ta jihar Kano Dakta Ali Haruna Makoda, ya kai ziyar bazata makarantar sakandare ta maza dake yankin Gano a Karamar hukuma dawakin kudu.

Kwamishina ya kai wannan ziyarae ce a wani yunkuri na tabbatar da cewa an yi biyayya ga umarnin  gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf na ayyana ranakun 5 da 6 ga watan Janairu, 2025 a matsayin ranakun da ɗalibai za su koma makarantu, domin fara zangon karatu na biyu na shekarar 2024/2025.

Dakta Ali Haruna Makoda ya koka kwarai da gaske kan yadda ya samu karancin dawowar ɗalibai harma da wasu malaman.

Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin magance dukkanin matsalolin da ake fuskanta a wasu daga cikin makarantun sakandire da na firimare da suke faɗin jihar.

Daga cikin makarantun da Kwamishinan ya ziyarta akwai Sakandiren Maza ta G.S.S Gano, da Sakandiren Maza ta kwana ta G.S.C.S Wudil, da kuma makarantar Sakandiren ƴan mata, ta kwana wato G.G.S.S Ƴargaya.

Dokta Ali Haruna Makoɗa, ya kuma nuna takaicin sa kan yadda ya tarar da shugabannin makarantar Sakandiren Maza ta G.S.S Gano, suka nuna halin ko in kula wajen kula da makarantar da kuma ƙarancin fitowar malamai da kuma ƙarancin zuwan ɗalibai makarantar.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai