Hukumomin tsaro a Najeriya sun cafke wani kasurgumin dan ta’adda mai satar mutane ya karbi kudin fansa da aka jima ana nema ruwa a jallo a sansanin alhazai da ke Abuja.
Jami’an tsaro ta tabbatar wa wakilin jaridar Aminiya cewa an kama wanda ake zargin, mai suna Yahaya Zango, yayin da ake tantance takardun maniyyatan da ke shirin tafiya Ƙasar Saudiyya domin aikin Hajji.
Yahaya Zango yana zaune ne a unguwar Paikon-Kore da ke Ƙaramar Hukumar Gwagwalada Abuja.
Majiyar ta ce mutumin ya zo da fasfonsa tare da sauran maniyyatan Abuja, amma jami’an hukumar DSS suka gane shi kuma suka cafke shi nan take suka tafi da shi domin cigaba da bincike.
Wani babban jami’i daga hukumar jin daɗin alhazai ta Abuja da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya tabbatar da kama shi, amma.
An ce hukumomin tsaron Najeriya sun daɗe sana nemansa kafin daga bisani aka yi nasarar cafke shi a yau, yana shirin tafiya aikin Hajji.

