Fitaccen malamin Musulunci Sheikh Isa Ali Pantami ya ƙalubalanci masu da’awar cewa a baya ya ce shiga siyasa haramun ne da su kawo shaidar abin da suke iƙirarin.
Sheikh Pantami wanda ya kasance tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, ya jefa wannan ƙalubale ne bayan da ya bayyana aniyarsa ta neman tsayawa takarar kujerar Gwamna a Jihar Gombe.
Fitaccen malamin ya yi zargin cewa yawanci mutane sukan yanko wasu maganganunsa su haɗa da wasu su yaɗa, domin cimma wani burinsu.
Pantami ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da BBC Hausa ya yi da shi, inda ya ce, ya shiga siyasa ne domin kawo shugabanci nagari a Najeriya.
A cewarsa tsohon ministan, mutane da dama ne suka fara kiran sa da ya fito takarar gwamna duk da yana ƙi a baya.
Ya ƙara da cewa amma a yanzu baya ga addu’o’i da neman yardar Allah an fara rinjayar sa