Abba kaɗai ke da takarar kai-tsaye a Kano —APC

Jam’iyyar APC ta saya wa Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano fom ɗin neman tazarce babu hamayya a zaɓen shekarar 2027 da ke tafe.

Shugabannin Jam’iyyar APC sun ɗauki wannan mataki ne bayan sun rungumi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Abba a matsayin ’yan takara babu hamayya a kujerar shugaban ƙasa da na Gwamnan Jihar Kano a zaɓen na 2027.

APC ta amince da takarar Tinubu da Abba babu hamayya ne bayan Rabiu Suleiman Bichi ya gabatar da ƙudurin a yayin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka gudanar a Gidan Gwamnatin Jihar Kano a ranar Alhamis.

Tsohon Gwamnan Jihar kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ne ya sanar da haka, tare da miƙa wa Gwamna Abba fon din takarar neman wa’adi biyu da jam’iyyar ta saya masa.

Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, ya bayyana cewa shugabancin jam’iyyar reshen Jihar Kano ya so ya saya wa Shugaba Tinubu fom ɗin takarar, domin tabbatar masa da goyon bayansu a gare shi, amma aka riga su.

“Mun so a ce mu daga Kano muka saya wa Tinubu fom ɗin takarar, amma sai muka ga wasu sun riga, amma babu damuwa, duk ɗaya ne,” a cewar Doguwa.

Duk da takarar babu hamayya da Tinubu da Abba suka samu, Ganduje ya bayyana cewa jam’iyyar APC Reshen Jihar Kano ba ta amince da bayar da tikitin takarar kai-tsaye ga masu neman sauran kujeru ba a zaɓen 2027.

Ya bayyana cewa a maimakon haka, APC ta amince a yi sulhu tsakanin masu neman takara domin tabbatar da adalci da kawar da ruɗani a cikin jam’iyyar.

Post masu alaƙa

An harbe ɗan bindiga a rukunin gidajen sojoji a Abuja

INEC ta mayar da sunan David Mark matsayin shugaban ADC a shafinta

Zulum ya bayyana Gubio a matsayin wanda ya fi so ya gaje shi