Sojoji sun harbe wani ɗan bindiga har lahira, bayan gungun ’yan ta’adda sun kai hari da nufin sace wani ɗan kasuwa a rukunin gidajen sojoji na Phase 5 da ke Kurudu a Abuja.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:47 na dare a ranar Alhamis, lokacin da ’yan bindigar su bakwai dauke da bindigogi ƙirar AK-47 suka tsallake katanga suka shigo rukunin gidajen ta baya.
Shigar su ke da wuya, sai suka fara harbi babu kakkautawa, lamarin da ya jawo hankalin sojoji da ke gadi a bakin ƙofar shiga, waɗanda suka mayar da martani nan take.
Wani mazaunin da ke kusa da gidan sojoji, Micheal Moses, ya shaida wa wakilinmu ta waya cewa sojoji tare da ’yan sanda na Kurudu sun yi musayar wuta da ’yan bindigar, inda suka kashe ɗaya daga cikin su.
Ya ce ɗaya daga cikin ’yan bindigar ya tsere da raunukan harsashi tare da sauran abokan aikinsa guda biyar a yayin musayar wutar.
A cewarsa, sojoji da ’yan sanda sun yi nasarar hana garkuwa da wani attajiri da ke zaune a rukunin gidajen, wanda shi ne ainihin burin ’yan bindigar.
“Gaskiya, daga abin da na ji daga abokina da ke zaune a wurin, ’yan bindigar su bakwai ne suka zo da niyyar yin garkuwa da wani babban mutum da ke zaune a rukunin gidajen, amma sojoji da ’yan sanda na Kurudu sun fatattake su, suka hana hakan,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa an ɗauke gawar wanda aka harba a cikin motar ’yan sanda, sai dai bai iya tabbatar da inda aka kai ta ba.
Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ’yan sanda ta Abuja, SP Adeh Josephine, ta tabbatar da yunkurin garkuwa da mutane a rukunin gidajen sojoji na Kurudu da wasu da ake zargin ’yan bindiga ne suka yi.
Ta bayyana cewa ’yan sanda suna ci gaba da binciken lamarin.