Hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta mayar da sunan Sanata David Mark matsayin shugaban jam’iyyar ADC a shafinta na intanet.
Matakin na zuwa ne bayan hukuncin Kotun Kolin ƙasar da ya soke hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ya buƙaci INEC ta cire sunan Davida Mark ɗin daga shafinta.
A ranar Alhamis ne Kotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar da shugabancin jam’iyyar ADC ɓangaren Sanata David Mark.
A hukuncin da kotun ta yanke ƙarƙashin mai shari’a Mohammed Lawal Garba, ta ce masu ƙarar su koma babbar kotun tarayya domin ci gaba da shari’ar da ake yi.
Alƙalan sun kuma yi watsi da hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke na cewa a tsaya inda ake a shugabancin ADCn kafin shigar da ƙara da NAfiu Bala Gombe ya yi a gaban Babbar Kotun Tarayya.