Shugaban Najeriya da Mataimakinsa sun taya Musulmi Murnar Maulidi
Yayin da al’umar musulmi ke murnar zagayowar ranar haihuwar annabi Muhammad (SAW), Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shattima sun bukaci
Yayin da al’umar musulmi ke murnar zagayowar ranar haihuwar annabi Muhammad (SAW), Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shattima sun bukaci
A ƙoƙarinsa na tabbatar al’ummar Kano sun samu labarai game da ayyukan gwamnatinsa, gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin karin masu taimaka masa na musamman a matsayin masu ɗaukar rahoto a ma’aikatu da hukumomi daban-daban na jihar Kano.
Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya gabatar wa majalisar dokokin jihar Kano ƙwarya-ƙwaryar kasafin kuɗi na fiye da Naira biliyan 58.
BY: YASIR ADAMU Ba wa ‘yan kasuwa damar gina matatun man fetur ko kuma farfado da na gwamnati shi ne mafita ga irin kwan-gaba-kwan-baya da ake samu game da farashin man fetur Nijeriya. Shugaban kungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu shiyyar Arewa, Alhaji Musa Yahaya Mai Kifi, ne ya bayyana haka yayin wata hira […]
Shugaban ƙungiyar malaman jami’a, ASUU, farfesa Emmanuel Osodeke, Ya ce matuƙar gwamnatin tarayya ta gaza dakatar da yuwuwar cigaba da ƙaruwar kuɗin makaranta ba a jami’o’in ƙasar nan, akwai yuwuwar kaso 40 zuwa 50 na ɗalibai za su gaza cigaba da karatu daga nan zuwa shekaru biyu masu zuwa.
Jam’iyyar NNPP ta mayar da martani ga alkalan da suka yi hukunci kan zaɓen gwamnan jihar Kano da aka yi a baya-bayan nan da suka ayyana magoya bayan jam’iyyar da ‘yan daba waɗanda suka yi wa rayuwarsu barazana.
Izuwa yanzu dai babu wani cikakkun bayanai game da dalilin wannan gobara, sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa tuni jami’an kashe gobara suka hallara a wurin domin kashe wutar.
Bayan gabatar da wasu daga cikin ababan tarihi da nasarorin ƙasar ta saudiya ne, maigirma Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bayyana godiyarsa ga ƙasar ta Saudiya bisa gudummuwar da ta bai wa Kano ta fannin kiwon lafiya, noma, ilimi da samarda ruwan sha a jihar.
Ministan Lantarki ƙasar nan Bayo Adelabu ya ce gwamnatin tarayya na ƙoƙarin haɓaka wutar lantarki ta kai migawat dubu 20 nan da shekarar 2026, kuma ta kai har migawat dubu 60 nan da shekarar 2060.
Gwamnan jihar Zamfara, Sauda Lawal Dare, ya umarci jami’an tsaro da su ɗauki tsattsauran mataki kan masu haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.