Shugaba Tinubu Ya Jaddada Kudirinsa Na Murkushe Ta’addanci A Nijeriya
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta samu ci gaba sosai wajen magance matsalar rashin tsaro a faɗin ƙasar cikin shekaru biyu da suka gabata. Shugaban ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa na daƙile ayyukan ta’addanci da kuma tabbatar da zaman lafiyar ƙasa. A wata sanarwa da Tinubu ya fitar a shafinsa na sada […]