Tinubu ya tura Badaru Neja saboda matsalar sace ɗalibai
Gwamnatin Najeriya ta tura babban ministan tsaron ƙasar, Muhammad Badaru Abubakar, zuwa jihar Neja inda aka sace ɗalibai ‘fiye da 200’. Ƙaramin ministan tsaron ƙasar, Muhammed Bello Matawalle ne ya bayyana haka ranar Juma’a da maraice a cikin shirin Ra’ayi Riga na BBC Hausa. ”Shi ma Badaru zai je Neja kamar yadda aka turoni Kebbi, […]