Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya a jihar Kano ta ce ta kama aƙalla mutum ɗari biyu da talatin da ake zargi da laifukan da ke da alaƙa da ƙwayoyi, tare da ƙwace muggan ƙwayoyi masu tarin yawa.
Shugaban hukumar a Kano, Abubakar Ahmed ne ya sanar da ci gaban a yayin wata ganawa da yayi da ƴan jarida a jihar.
Ya ce hukumar ta sami wannan nasarar ce a yaƙin da take yi da ta’ammuli da ƙwayoyi a wani s aikin kame da ta yi na kwanaki 30 a faɗin jihar ta Kano.
Ya ce sun gudanar da aikin kamen ne tare da haɗin gwiwar ƴan sandan ƙasar, da hukumar tsaro ta civil defence, da hukumar kula da shige da fice, da jami’an tsaron farin kaya (DSS) ƙarƙashin wata rundunar haɗin gwiwa ta dawo da zaman lafiya da gyara halayyar matasa.
A cewar sa, sun shafe tsawon wata guda suna kai samame a sannanun matattarar masu ta’ammuli da miyagun ƙwayoyi da ke Kofar Ruwa da Tashar Rami da Rijiyar Lemo da Kurna da Zage da Dorayi Karshen Waya da Dawanau da Filin Idi da Rimi Market da Zango da Kano Line da Kofar Mata da wasu wuraren.
Shugaban hukumar ya kuma ce tuni kamen da suka yi ya kawo sauƙin aikata wasu laifuka kamar ƙwacen waya da dabanci da wasu laifukan.