Janar Christopher Musa ya bayyana jiragen a matsayin waɗanda za su kawo sauyi wajen tunkarar barazanar matsalolin tsaro a Najeriya.
Ya jaddada muhimmacin samar da hanyoyin tsaro na soji a cikin gida, da kuma ƙalubale a siyasar duniya wajen samar da kayyakin tsaro.
‘‘Jiragen za su taka muhimmiyar rawa wajen haɓaka ayyukan sojojinmu, musamman a duniyar da samar da kayyakin aikin soja na zamani ke cike da ƙalubale saboda siyasar duniya.’’
“Idan ba ku samar da abin da kuke buƙata ba, za ku kasance a ƙarƙashin wasu, ko da kuna da albarkatun kuɗi don samun su,” in ji shi.
Janar C Musa ya ƙara da cewa jiragen za su taimaka wa Najeriya wajen daukar matakan gaggawa don fuskantar kalubalen tsaro, tare da rage dogaro da kayayyakin ƙasashen ƙetare.

