An Ƙaddamar Da Jiragen Yaƙi Mara Matuƙa Da Aka Kera A Najeriya 

Rundunar sojin Nijeriya ta yi bikin ƙaddamar jiragen yaƙi marasa matuƙa da aka ce an ƙera a kasar a karon farko kuma mafi girma a nahiyar Afirka baki ɗaya.

Kafar yaɗa labarai ta TRT Africa ta ce an ƙera jiragen ne tare da haɗin gwiwar kamfanin Briech USA na Amurka da ke da ofis a Abuja.

A yayin bikin kaddamar da jirgin da aka yi a hedikwatar ta Briech UAS da ke Abuja a ranar Laraba, Babban Hafsan Hafsoshin Tsaro Najeriya, Janar Christopher Musa ya bayyana shirin a matsayin wani muhimmin mataki a tafiyar Najieriya wajen dogaro da kai a fasahar tsaro da inganta tsaro.

Janar Christopher Musa ya bayyana jiragen a matsayin waɗanda za su kawo sauyi wajen tunkarar barazanar matsalolin tsaro a Najeriya.

Ya jaddada muhimmacin samar da hanyoyin tsaro na soji a cikin gida, da kuma ƙalubale a siyasar duniya wajen samar da kayyakin tsaro.

‘‘Jiragen za su taka muhimmiyar rawa wajen haɓaka ayyukan sojojinmu, musamman a duniyar da samar da kayyakin aikin soja na zamani ke cike da ƙalubale saboda siyasar duniya.’’

“Idan ba ku samar da abin da kuke buƙata ba, za ku kasance a ƙarƙashin wasu, ko da kuna da albarkatun kuɗi don samun su,” in ji shi.

Janar C Musa ya ƙara da cewa jiragen za su taimaka wa Najeriya wajen daukar matakan gaggawa don fuskantar kalubalen tsaro, tare da rage dogaro da kayayyakin ƙasashen ƙetare.

Post masu alaƙa

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 26 a Borno

Tinubu ya tafi hutun mako uku

Gwamnatin Kwara ta haɗa mutum 146 da aka sace a Woro da iyalansu