An yi kira ga hukumomin tsaro da sauran al’umma, su kara azama wajen karanta alkur’ani mai girma da kuma sanin ma’anarsa.
Limamin masallacin juma’a na Kofar Gadon Kaya, Sheik Aliyu Yunus, ne ya bayyana hakan yayin bude musabakar karatun alkur’ani mai girma, da aka shirya tsakanin hukumomin tsaro dake jihar Kano.
Rundunar yan sandan jihar Kano,ce ta shirya musabukar tsakaninta da sauran hukumomin tsaron dake aiki a jihar, don kara zaburar da su wajen yawaita karanta alkur’ani mai girma.
Babban limamin masallacin juma’a na shelkwatar rundunar yan sandan Kano, CSP Abdulkadir Haruna, ya bayyana cewa sun shirya musabakar don kara samun hadin kai tsakaninsu da abokan aikinsu da kuma tunatar dasu karanta alkur’ani mai girma don kar aikinsu yah ana su karantawa.
- Gwamnan Kano Abba Kabir Ya ziyarci Yankunan Da Yan Bindiga Ke Yiwa Barazana
- Gwamnan Abia ya ziyarci Tinubu a Villa
Mukaddashin kwamishinan yan sandan jihar Kano, DCP Lawan Isah Mani, sh ine ya wakilci mataimakin shugaban yan sandan Nijeriya mai kula da shiya ta daya Kano, da kwamishinan yan sandan Kano, ya bayyana cewa duk wanda yake musulmi dole ne ya yi farin ciki da hakan domin alkur’ani shi ne turbar rayuwa.
Da yake gabatar da nasiharsa ga jami’an tsaron limamin masallacin juma’a na Kofar Gadon Kaya, Sheik Aliyu Yunus, ya ce Allah ya saukar da alkur’ani da shari’a wacce take kare abubuwa guda biyar, kuma duk musulmi yana da kyau yasan alkur’ani da sanin ma’anarsa.
Suma wasu daga cikin jami’an tsaron da suka shiga musabakar sun bayyana farin ciki da kuma burunsu na samun nasara
Mutane 41 ne suka shiga musabakar daga hukumomin tsaron jihar.