Rundunar ’Yan Sandan Najeriya A Jihar Kano, ta sanar da kama wani babban ɗan fashi da makami.
Mai magana da yawun rundunar a Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana cewa sun kama mutumin da ake zargin ƙasurgumin ɗan fashi ne.
An sami ɗan fashin da kuɗi kimanin Naira miliyan 4 da dubu ɗari 9 da tamanin.
Kazalika an samu a samu bindiga ƙirar AK-47 guda biyu da kuma alburusai 47.
- Yadda Saurayin Mai Awara Ya Mata Wanka Da Tafasasshen Mai
- An Bukaci Tinubu Ya Dauki Matakin Gaggawa A Najeriya
‘Yan Sanda sun yi nasarar kama ɗan fashin ne da ƙarfe 6 na safiyar ranar Talata ne.
SP Haruna Kiyawa ya bayyana kama ƙasurgumin ɗan fashin mai suna Hassan Iliya, mai shekara 35 da ke Alhazawa a ƙaramar hukumar Musawa ta Jihar Katsina