An Naɗa David Mark A Matsayin Shugaban Jam’iyyar ADC

Ƙusoshin adawa a Najeriya sun bayyana tsohon shugaban Majalisar Dattijan ƙasar David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), wadda suka amince da ita a matsayin jam’iyyar haɗaka.

Ƴan adawar sun ɗauki wannan mataki ne a taron da suka gudanarwa a Abuja, babban birnin Najeriya.

A jerin tattaunawar da suka gudanar na baya-bayan nan manyan masu adawa da gwamnatin ƙasar sun amince da ADC a matsayin jam’iyyar da za su yi amfani da ita domin ƙalubalantar shugaban ƙasar Bola Tinubu a babban zaɓe na shekarar 2027.

A wajen taron na yau Laraba an samu halartar manyan ƴan adawa da suka hada da Atiku Abubakar da Peter Obi da Nasir El-Rufa’i da sauran su.

Post masu alaƙa

Kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin shekaru 490 ga tsohon shugaban bankin NEXIM.

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wanda ake zargi da damfarar mutane da cewa shi babban jami’in Dan sandan ne.

Hisbah ta fara horas da sabbin jami’anta a Jigawa