Babbar Sallah: Gwamnatin Kano Ta Shawarci Al’umma Su Duba Lafiyar Dabbobin Layyarsu.

Daga: Zubaida Abubakar Ahmad

Gwamnatin Jihar Kano ta bukaci jama’a da su tabbatar da cewa dabbobin da za su yi layya da su ba su dauke da wata cuta kafin Babbar Sallah.

Kwamishinan Lafiya na Jihar, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, inda ya ce hakan zai taimaka wajen kare lafiyar jama’a da kuma dakile yaduwar cututtuka.

Ya ce akwai wasu cututtuka da dabbobin ke dauke da su da za su iya yaduwa ga mutane, musamman idan ba a kiyaye tsafta ba wajen yanka da dafawa.

Dakta Labaran ya bukaci mata da masu dafa abinci da su tabbatar sun wanke naman da ruwa mai tsafta tare da dafa shi sosai kafin ci, domin hakan zai taimaka wajen hallaka kwayoyin cuta da ke iya kasancewa a cikin naman.

Ya kara da cewa gwamnatin Jihar Kano ta riga ta tanadi magunguna da kayan agaji a asibitocin gwamnati domin tunkarar duk wata matsala da ka iya tasowa yayin bukukuwan Sallah.

Kwamishinan ya ce Ma’aikatar Lafiya za ta ci gaba da wayar da kan jama’a kan hanyoyin kiyaye lafiya, musamman a irin wannan lokaci da yawan cin nama ke karuwa.

A karshe, ya yi fatan al’ummar Kano za su gudanar da bukukuwan Sallah cikin kwanciyar hankali da lafiya.

Post masu alaƙa

Sojojin Najeriya sun daƙile yunƙurin garkuwa da mutane tare da ceto mutum 23

Dan KAROTA da direba ya buge ya gudu Nasiru Abdullahi Mai Jihadi ya rasu ya bar mata 2 da ‘ya’ya 12.

An kama budurwa ‘yar shekara 15 kan safarar miyagun kwayoyi a Delta.