Gwamnatin Kano Ta Faɗi Ranar Komawa Makaranta
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana ranakun 6 da kuma 7 a matsayin ranakun komawa makaratun Furamare da sakandare domin cigaba da Karatun Zango na Uku na shekarar 2024/2025.
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana ranakun 6 da kuma 7 a matsayin ranakun komawa makaratun Furamare da sakandare domin cigaba da Karatun Zango na Uku na shekarar 2024/2025.
Dubun wasu ɓarayin yara ta cika bayan an kama su da satan yara daga jihar Taraba dake Arewa Maso Gabashin Najeriya zuwa kudu maso gashin ƙasar.
Rahotanni daga jihar Filato na cewa adadin mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren baya-bayan nan a ƙaramar hukumar Bokkos sun kai 52.
Kotun Ƙoli ta soke hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja, ta yanke wanda ya amince da Julius Abure a matsayin shugaban jam’iyyar LP na ƙasa.
Dubban Mutane daga sassan Najeriya ne suka Halarci Jana’izar Shaik Abdul’aziz Idris Dutsen Tanshi wanda Allah ya yi wa rasuwa a daren Alhamis.
Tsohon mai magana da yawun kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya Dokta Hakeem Baba-Ahmed, ya yi murabus daga matsayin mai bai wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin siyasa.
Daga : Safiyanu Haruna Kutama Fitaccen malamin addinin Islama da ke Jihar Bauchi, Dokta Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya riga mu gidan Gaskiya. Makusantan malamin sun tabbatar da rasuwarsa , Inda ya shafe tsawon lokaci Yana karantarwa da kuma harkar kasuwanci. Malamin ya yi fama da rashin lafiya inda gabanin watan Ramadana ya fita neman […]
A ranar Alhamis ɗin nan ne rundunar sojin Nijeriya ta ce ana cigaba da farautar ƙasurgumin ɗanbindiga, Kachalla Bello Turji wanda sojojin ƙasar suka daɗe suna nema sun ce ya kusa komawa ga mahalicci. Rundunar ta bayyana cewa kuma kwanakinsa sun kusa ƙarewa. Ta kuma yi watsi da iƙirarin da ake na cewa sojoji sun […]
Cibiyar yaƙi da ta’addanci ta ƙasa (NCTC) ta miƙa tsohon Darakta-Janar na masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), Birgediya Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya) ga mai ba shugaban ƙasa shawara kan sha’anin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu. Tsiga, wanda aka kuɓutar bayan ya kwashe kwanaki 56 a tsare, a ranar Laraba an miƙa shi ne tare […]
Jami’an hukumar kashe gobara reshen jihar Kano da kuma na gwamnatin tarayya sun samu nasarar shawo kan gobarar data tashi a jami’ar Northwest dake jihar . Shugaban hukumar kashe gobara na jihar Kano, Sani Anas , ne ya tabbatar da hakan, lokacin da yake yi wa manema labarai karin haske kan musabbabin tashin gobarar. Anas, […]