Kwankwaso da Dickson sun gana kan rikicin NDC a Kano

Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya gana da Jagoran Jam’iyyar na ƙasa, Sanata Seriake Dickson, a gidansa da ke Guzape a Abuja ranar Talata. Taron ya samu halartar ɗan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar, Kwamared Aminu Abdussalam, da Shehu Wada Sagagi, Nasiru Garo da sauran manyan jagororin NDC. […]

Read more

Sojoji sun ceto mutane 47 da ISWAP ta yi garkuwa da su a Borno

Rundunar haɗin gwiwa ta sojojin Najeriya a Arewa maso Gabas, wato Operation Hadin Kai, ta ce ta ceto mutane sama da 47, akasarinsu mata da yara, daga hannun ‘yan ta’addan ISWAP a jihar Borno. Jami’in yaɗa labaran rundunar, Kyaftin Mohammed Goni, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata a Maiduguri. […]

Read more