Labarai

Babban Labari

Rundunar ƴan sandan Nijeriya shiya ta ɗaya ta tsaurara tsaro gabanin Babbar Sallah

Rundunar ƴan sandan Nijeriya shiya ta ɗaya dake jihar Kano, ta bayyana cewa ta ɗauki tsauraran matakan tsaro, kamar yadda babban sufeton ƴan sadan Nijeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu, ya bayar da umarni, don tabbatar da an gudanar da bukukuwan babbar sallah cikin kwanciyar hankali da lumana. Mataimakin sufeton ƴan sandan Nijeriya shiya ta ɗaya, […]

Babban Labari

An kama mutum 4 kan damfarar maniyyata a Kebbi

Wasu mutum huɗu da ake zargi da damfarar maniyyata aikin Hajjin bana sun shiga hannu a Jihar Kebbi. Jami’in hulɗa da jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi ta, SP Bashir Usman, ya bayyana cewa dubun waɗanda ake zargin ta cika ne bayan ƙorafe-ƙorafe daga waɗanda abin ya shafa da kuma Hukumar Jin Daɗin Alhazai […]

Babban Labari

Hukumar Road Safety Za Ta Ɗauki Tsattsauran Matakai Kan Masu Tuƙin Ganganci A Kano.

Hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa reshen jihar Kano, ta ƙudirin aniyar ɗaukan tsattsauran mataki ga duk wanda aka kama da laifin yin tuƙin ganganci a lokutan bukukuwan babbar sallah. Jami’in hulɗa da jama’a da wayar da kai na hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa reshen jihar Kano, CRC Abdullahi Labaran, ne ya bayyana hakan yayin tattaunawarsa […]

Babban Labari

Majalissar dinkin duniya ta ce miliyoyin mutane a Najeriya na iya fuskantar matsananciyar yunwa

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa miliyoyin ’yan Najeriya na iya fuskantar matsananciyar yunwa a watanni masu zuwa sakamakon matsalar tsaro, rikice-rikice da kuma tsadar rayuwa da ke ƙaruwa a faɗin ƙasar. Hukumar kula da ayyukan jin-ƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya (OCHA), ta ce iyalai da dama za su shiga wani yanayi da ka […]

Babban Labari

Ebola: An dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a Congo

Hukumomi a Jamhuriyar Dimokraiyyar Kongo sun dakatar da zirga-zirgar jiragen sama zuwa yankin Bunia babban binin Ituri har illa masha Allahu, saboda barazanar yaduwar cutar Ebola. Sanarwa daga ma’aikatar sufurin ƙasar ta nuna cewa za a tantance jiragen kayan jin ƙai, da na ma’aikatan lafiya, kuma za a bukaci izini daga hukumomin lafiya da na […]

Babban Labari

Ɗan Ganduje Ya Sayi Fom Ɗin Takarar Majalisar Tarayya A NDC

Abdulaziz Umar Ganduje, babban ɗan tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya sayi fom ɗin takarar kujerar Majalisar Tarayya a ƙarƙashin jam’iyyar NDC. Zai tsaya takarar ne a mazaɓar Dawakin Tofa/Tofa/Rimin Gado da ke Jihar Kano. Duk da kasancewar mahaifinsa a jam’iyyar APC, Abdulaziz, ya daɗe yana bin siyasar Kwankwasiyya kuma yana […]

Babban Labari

Hukumar tsaron farin kaya ta Civil Defence  (NSCDC) reshen jihar Gombe, ta kama wasu mutane biyar da ake zargi da hannu a ƙungiyoyin satar babura da na’urorin lantarki a sassa daban-daban na jihar. Kamen ya biyo bayan wasu samame da jami’an hukumar suka gudanar bisa bayanan sirri a ƙananan hukumomin Billiri da Balanga da Akko […]

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai