Labarai

Babban Labari Labarai

An gano wurin da ’yan Boko Haram suke ɓoye man fetur a ƙarƙashin ƙasa

Rundunar Operation Haɗin Kai ta Sojin Nijeriya ta sanar da gano wani wuri da mayaƙan ƙungiyar Boko Haram ke ɓoye man fetur, magunguna da sauran kayayyakin aikinsu a ƙarƙashin ƙasa. Samun wannan nasarar na zuwa ne bayan jerin samamen da dakarun rundunar Operation Desert Sanity suka kai a yankunan Timbuktu Triangle da ke Jihar Borno. […]

Babban Labari Labarai

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana dalilan dake janyo rashin zartar da hukunci.

Kwamishinan shari’a na jihar Kano Barista Abdulkarim Kabiru Maude, SAN, ne ya bayyana hakan yayin zantarwarsa da wakilin mu yau litinin. Wannan dai na zuwa bayan kisan gillar da aka yi wa wata matar aure da ƴaƴanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi, lamarin da ya jefa al’ummar jihar Kano cikin alhini. ‘’ da zaka ga hukunce-hukuncen […]

Babban Labari Labarai

Tinubu ya yi alhinin rasuwar ɗan kasuwar Kano Bature Abdulaziz

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhini da jimami kan rasuwar fitaccen ɗan kasuwa kuma jagoran al’ummar ’yan kasuwa a Jihar Kano, Alhaji Bature Abdulaziz, wanda ya rasu a ƙarshen mako. Cikin wata sanarwa da fadarsa ta fitar, Tinubu ya miƙa ta’aziyyarsa ga al’ummar ’yan kasuwa a Kano da iyalan marigayin, da gwamnatin Jihar […]

Babban Labari Labarai

NBRP ta yi alkawarin hada kai da hukumar NOA don kara sanya son karatu ga yan Nijeriya

Hukumar wayar da kan al’umma ta ƙasa NOA tare da hadin gwiwa da Gamayyar Ƙungiyoyin Haɗin Kan Makaranta Littattafai da Raya Al’adar Karatu wanda a turanci ake kira Network of book club and reading culture suka yi tsari domin gina son kararu tare da samun Ingantaccen ilimi ga ‘yan kasa. ‎ ‎Da yake jawabi Amadadin […]

Babban Labari Wasanni

Senegal ta lashe gasar AFCON ta 2025

Senegal ta zama zakarar Gasar Nahiyar Afirka (AFCON) ta 2025, bayan doke mai masaukin baƙi, Maroko da ci ɗaya mai ban haushi a wasan ƙarshe na gasar. Ɗan wasan tsakiyar Senegal, Pape Gueye ne ya jefa ƙwallo ɗaya tilo a raga a minti na 94, bayan shafe minti 90 ba tare da zura ƙwallo a […]

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000